Ummara: Ƴan Birtaniya 5 sun yi tattaki da ga Makka zuwa Madina

0
394

Wasu mutane biyar da ga kasar Biritaniya sun kammala tattaki daga Makka zuwa Madina.

Sun bayyana cewa sun yi hakan ne bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) lokacin da ya yi Hijira.’ da ga Makka zuwa Madina

Mahajjatan Ummaran sun yi tattaki na tsawon sa’o’i 185, inda su ka yi tafiyar kusan kilomita 550 daga Makka zuwa Madina don ganin sun aikata irin abin da Annabi Muhammad (s.a.w) da sahabbansa su ka sha fama fiye da shekaru 1400 da suka gabata.

“Bibiyar tafarkin Annabinmu (SAW) kamar zama da tafiya tare da shi ne.

“Mun koyi abubuwa da yawa game da shi, kuma soyayyarmu gare shi ta na rubanya wamai yawa,”. Inji Rashid Ali, ɗaya daga cikin mahajjatan Ummarar.