Yarjejeniyar Hajjin 2023: NAHCON ta yaba wa Saudiyya kan haɗin-kai da ta baiwa Nijeriya

0
292

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta yi godiya ga hukumomin Saudiyya dangane da haɗin kan da su ka bai wa tawagar Najeriya da suka ziyarci ƙasar kwanan nan don rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MOU) tare da kamafnoni da dama game da Hajjin 2023.

Sbugaban NAHCON na ƙasa, Zikirullah Kunle Hassan ne ya miƙa godiyar mai taken “Godiya ga Nasarar Rattaba Hannu ” wanda ya fitar a yau Litinin.

Shugaban ya ce: “A madadin tawagar Nijeriya da ta ziyarci Masarautar Saudiyya kwanan nan domin rattaba hannun a Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) game da Hajjin 2023, ina miƙa godiya ga hukumomin Masarautar bisa haɗin kan da su ka bamu.

“Na yaba wa Mai Martaba kuma Hadimin masallatan Makka da Madina, Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud da Yariman Masarautar kuma Fira Ministan Saudiyya, Muhammad Bin Salman Al Saud, bisa muhimmancin da suka bai wa shirye-shiryen Hajjin na 2023.

“Amincewarsu babbar alama ce da ke nuni da nasara a Hajjin bana. Ko shakka babu almummar musulmin duniya na yabo da sadaukarwar da Masarautar kan yi wajen tabbatar da walwalar mahajjata a lokautan Hajji da Umarah.

“Haƙiƙa Najeriya tana cin moriyar kyakkyawar mu’amalar aiki tare da Saudiyya, mu a hukumar NAHCON shaida ne a kan haka,” in ji shi.

Zikirullah ya yi amfani da wannan dama wajen nuna godiya dangane rawar da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Zubair Dada da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Harkokin Waje, Sanata Adamu Bulkachuwa da takwaransa na Majalisar Wakilai kan harkokin Hajji, Honorabul Hassan Nalaraba, wajen ganin an cim ma nasarar a aikin Hajji mai zuwa.

Haka nan, ya ba da tabbacin NAHCON da ma’aikatanta za su aiki babu kama hannun yaro wajen tabbatar da ayyukan Hajjin bana sun gudana sumul ƙalau.