Hajjin 2023: Bauchi ta fara yi wa maniyyata rijista

0
520

Ta ayyana miliyan N1.5 mafi ƙarancin ajiyar da za a fara biya

Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi ta sanar da cewa, Gwamnan jihar, Bala Abdulkadir Muhammad, ya amince ta fara yi wa maniyyata Hajjin bana da Umarah a jihar rijista.

Kazalika, hukumar ta sanar cewar, miliyan N1.5 zuwa miliyan N2 shi ne mafi ƙarancin kuɗin ajiyar da aka amince maniyyatan jihar su fara biya game da Hajjin 2023 kafin lokacin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) za ta sanar da ainihin kuɗin kujerar Hajjin bana.

Kazalika, hukumar ta ce miliyan N1 shi ne mafi ƙarancin abin da maniyyata Umarah a jihar za su fara biya yayin Ramadan na bana.

Hukumar ta shawarci maniyyatan da lamarin ya shafa da su ziyarci Sakatariyar Hukumar da ke Hanyar Adamu Jumba don karɓar takardar biyan kuɗi a banki (Teller).

Haka nan, hukumar ta ayyana Laraba, 25 zuwa Asabar 28 ga Janairu a matsayin ranakun da maniyyata Hajji za su ziyarci hukumar don karɓar tasu takardar biyan kuɗi a banki.

Ta ƙara da cewa, Laraba, 1 zuwa Asabar, 4 ga Fabrairu su ne ranakun da aka tsayar domin maida takardun ‘Teller’ da aka cike wanda bayan haka za a tafi a karɓi risit a sakatariyar hukumar ko hedikwatar ƙananan hukumomin jihar.

Ta ce ba za ta lamunci duk wata hada-hadar da ta saɓa wa tsarin da aka amince da shi ba.

Tare da kira ga baki ɗayan maniyyatan jihar da su bai wa hukumar haɗin kan da ya dace don cim ma nasara.