Hajjin 2023: Jordan ta fara rijistar maniyyata ta yanar-gizo

0
331

Ma’aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci da wuraren tsarki a kasar Jordan ta fara rijistar farko ga masu son zuwa aikin Hajjin bana na shekarar 1444 Hijira/2023 ga ‘yan kasarda mazauna yankin zirin Gaza.

Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya, Talata, cewa za a yi rajista ta shafin yanar gizo na Hajji (https://hajj.gov.jo) daga safiya har zuwa karfe 10 na dare ranar Talata 7 ga Fabrairu, 2023.

Ministan Awkaf da Al’amuran Addinin Musulunci da wurare masu tsarki Muhammad Al-Khalayleh ya ce wadanda ke son yin rajistar wadanda suka cika sharudda, za su biya dinari 200 ga tsofaffi da aka yi wa rijista kawai, kuma za a mayar musu da kuɗin su bayan kammala rajistar a daidai lokacin da Hukumar Hajji da Umrah ta kayyade.

Ministan ya bayyana cewa ba a bashi damar biyan wadanda su ke raka alhazai don yi musu hidima ba, yana mai nuni da cewa ana biyan kuɗin ta hanyar “e-fawateercom”, ko kuma ta ziyartar wani reshe na bankin Musulunci na kasar Jordan.

An buƙaci maniyyaci da zai biya kudin aikin Hajji na wannan shekara, ya zamana kada ya wuce shekarun haihuwa da ga 31 ga Disamba, 1960 ko ƙasa da haka, wanda kuma bai taɓa yin aikin Hajji ba, kuma ya sami allurai biyu na rigakafin cutar korona da aka amince.

Dangane da masu biya ta asusun Hajji, Ministan ya nuna cewa waɗanda su ka tanadi dinari 3,000 kafin farkon watan Satumba na 2017 suna da damar yin rajista ta shafin yanar gizon asusun (https://hajjfund.gov.jo