Hukumar Alhazai ta Katsina na kiran alhazan 2022 da su karɓi rarar kuɗinsu

0
211

Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta ce ta na ci gaba da sauraren wasu maniyyatan aikin Hajji na 2020 da 2021 da su zo su karɓi rarar kuɗaɗen su.

Kakakin hukumar, Badaru Bello Karofi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce alhazan da za su karɓi rarar ta su su ne wadanda su ka biya cikakken kuɗin Hajji na Naira miliyan 2.5.

Ya ce tarar kuɗin nasu Naira dubu 50,392.11 ne.

Ya yi kira ga maniyyatan da su gaggauta bayar da lambar asusun su ko ta amintattun su domin biyan kuɗaɗen na su.

Ya ƙara da cewa za su kai lambar asusun ne ga shiyyar da su ka biya kuɗaɗen Hajjin.