Saudiyya ta saka ranar da za a biya kashi na 2 na kuɗin Hajjin 2023 ga maniyyatan cikin ƙasar

0
348

Ranar lahadi 29 ga watan Janairu ne wa’adin biyan kashi na biyu na kudurorin gida na aikin hajjin bana mai zuwa, daidai da 7 ga watan Rajab.

Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta jaddada bukatar ƴan kasar da na kasashen ketare da su kammala biyan kashi ukun don tabbatar da an ajiye su da kuma ba su izinin aikin Hajji.

Abin lura ne cewa ma’aikatar ta bullo da hanyoyin biyu a bana na biyan kudin aikin Hajji ga mahajjatan cikin gida.

Na farko shi ne biyan kuɗin gaba ɗaya da zarar an yi ajiyar kuɗi, kuma da zarar an ba da daftari don biyan kuɗin, matsayin ajiyar ya zama “tabbace”.

Hanya ta biyu kuma ita ce biyan kudaden a kashi uku.

Ma’aikatar ta sanar a farkon wannan watan cewa alhazai na cikin gida su na da zaɓin biyan kudin aikin Hajji kaso uku, maimakon a biya gaba daya g kamar yadda ya faru a shekarun baya.