A kokarin daƙile matsaloli wajen gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji a Nijeriya, Cibiyar Horas da Aikin Hajji ta Najeriya (HIN) wata cibiya da ke karkashin kulawar Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), da aka kafa ta kwanan nan, ta nuna sha’awarta na yin hadin gwiwa da Hukumar Bunkasa Fasaha ta Ƙasa, NITDA akan kawo fasahar a shirye-shirye na aikin Hajji.
A wani taro da su ka yi a hedikwatar Hukumar NITDA da ke Abuja a jiya Juma’a, NITDA da HIN sun amince cewa irin wannan hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin biyu zai taimaka wajen karfafa aikin Hajji a kasar.
A nasa jawabin, babban daraktan hukumar NITDA, Kashifu Inuwa, CCIE, ya bayyana kafa cibiyar a matsayin muhimmaci wajen ilimantar da maniyyata, da kuma daidaita hanyoyin da za a bi wajen inganta shirye-shirye na aikin hajji a ƙasar.
Ya bayyana kafa Cibiyar HIN a matsayin wani al’amari a lokacin da ya dace da masu niyyar zuwa aikin Hajji ke bukatar a ilimantar da su, inda ya kara da cewa, “sabuwar cibiya an kafa ta a lokaci ne da ya dace da ku tsara dabarun ku, irin bukatun da ku ke son cimma. Ana buƙatar amfani tunani da basira wajen tafiyar cibiyar.”
Ya ce tsarin haɗin gwiwa tsakanin NITDA da Cibiyar wata babbar dama ce domin ƙungiyoyin biyu su na da buri ɗaya na ƙididdige ayyuka a cikin ƙasar da kuma samun amfani da fasahar zamani
Tun da fari, shugaban Cibiyar ta HIN, Farfesa Nasiru Muhammad Maiturare, ya ce abin da ya mayar da hankali a kai shi ne yin amfani da fasahar zamani wajen samar da hidimomi, musamman a halin yanzu da aka mayar da tsarin aikin Hajji ya zama na fasahar zamani.