Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Adamawa, Malam Abubakar Salihu ya gana da Jami’an Alhazai na Kananan Hukumomi.
Hajj Reporters ta jiyo cewa an yi ganawar ne domin yi musu bayani kan ci gaban da ya shafi aikin Hajjin bana.
Babban Sakataren ya bayyana wasu matakai da aka sanya don samun nasarar ayyukan Hajjin 2023, kamar yadda wata gajeriyar sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya fitar.