Tashin farashin Dala da na kayayyaki ne ya sanya ƙarin kuɗin aikin Hajji – Gwamnatin Indonesia

0
357

Gwamnatin Indonesiya ta dora alhakin karin kuɗin aikin Hajjin 2023 a kan tashin farashin dala da hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya ninka abin da mahajjata su ka biya a 2022.

Kwanan nan ne ma’aikatar harkokin addini ta yanke cewa matsakaicin kudin aikin hajji ga kowane mutum zai kai Rp miliyan 98.89 (kimanin dala 6,604) a bana.

Mutum zai bukaci ya biya Rp miliyan 69.1 don tafiya aikin hajji na bana, wani gagarumin kari a na Rp miliyan 39.8 a 2022.

Sauran Rp miliyan 29.7 za su fito ne daga dawo da kudaden da Hukumar Kula da Asusun Hajji ta ƙasar (BKPH) ke gudanarwa.

“Akwai abubuwa guda uku [wanda ya haifar da tashin gwauron zabi], da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki, dala, da kudin jirgi,” Jaja Jaelani, daraktan kula da asusun hajji a ma’aikatar kula da harkokin addini, ya fada a wani taron tattaunawa a karshen mako.

Jaja ya ce a 2022, dala ta kai Rp 14,000, amma sai ta tashi zuwa Rp 15,000 a bana. Canjin dala ne ya haifar da hauhawar farashin jirgi.

Sai dai a cewar Jaja, gwamnati na ci gaba da duba kudaden aikin hajjin bana. Har yanzu dai Majalisar Wakilai ba ta yanke shawarar karshe ba kan kudaden, amma da alama za ta kai ga kammalawa a wata mai zuwa.

“Wataƙila a tsakiyar watan Fabrairu, amma har yanzu ana tattaunawa,” in ji Jaja