Hukumar Jindadin Alhazan Jihar Katsina ta gudanar da taro don tsara shirin rijistar alhazai shirin rijistar maniyyatan Hajjin bana.
Hukumar ta gudanar da taron a shelkwatar ta da ke Katsina.
Taron ya hada da jami’an alhazai na ƙananan hukumomi da shugabannin shiyyoyi da mataimakansu.
Da ya ke jawabin maraba, Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, ya ce makasudin taron shi ne domin yin duba kan irin cigaban da aka samu a karbar kudin aikin Hajji daga kowace shiyyar jukumar.
A jawabinsa Bayan taron, Alhaji Kuki ya nuna gamsuwa da yadda shirin rijistar maniyyatan ke tafiya, tare da ba da umarnin ci gaba da jajircewa ga aikin domin samun nasararorin da ake bukata.
Kuki ya kuma nemi jami’an hukumar na shiyyoyi da su bayyana yanda ake ciki dangane da rijistar alhazan, kuma a ci gaba da karbar kudin ajiyar.
Haka kuma taron ya nuna gamsuwa a kan kokarin alhazai na 2020, 2021, da 2022 da suka biya cikakken kuɗin Hajji na Naira miliyan 2.5M, wajen kawo lambar asusun su na banki don maido musu da rarar kudin aikin Hajjin bara na Naira Dubu 50 da ɗoriya.