Hajjin 2023: Hukumar Alhazai ta Kano za ta yi bikin bude bitar Hajjin bana

0
281

Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta gayyaci maniyyata aikin Hajjin 2023 domin halartar bikin bude bitar mako-mako.

Hajj Reporters ta rawaito cewa an saba yin bitsr a ranakun Asabar da Lahadi.

A wata gajeriyar sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Hadiza Abbas Sanusi ta sanya wa hannu a Kano, za a ƙaddamar da bitar a ranar Asabar, 4 ga watan Febrairu.

Ta ce za a kaddamar ta bitar a babbar cibiyar bita da ke makarantar SAS, da kuma sauran cibiyoyi 15 na bita a jihar.

Sanarwar ta yi kira da maniyyata da su halarci taron kaddamarwar.