Hukumar alhazai ta Abuja ta buƙaci mamiyyata su cika kuɗin Hajjin su zuwa N2.5m

0
241

Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya Abuja, FCT, ta bukaci maniyyatan da su ka biya kasa da mafi karancin Naira Miliyan 2.5 na kuɗin Hajjin bana da su cikasa domin samun gurbin shiga aikin Hajjin shekarar 2023.

Hakazalika hukumar ta buƙaci maniyyatan da ba su samu damar zuwa aikin Hajjin bara ba da su garzaya su sabunta rajista da hukumar.

Daraktan Hukumar, Malam Muhammad Nasiru Danmallam ne ya ba da umarnin a lokacin da ya ke yi wa manyan jami’an gudanarwa bayanin ziyarar farko kafin aikin Hajji a Saudiyya da shirye-shiryen gudanar da ayyukan Hajji na 2023.

Mallam Muhammad Danmallam ya ce umarnin ya zama dole domin baiwa hukumar damar tattara ainihin jerin sunayen maniyyatan da za su gudanar da aikin a bana.

Daraktan ya kuma bukaci wadanda suka biya kudin aikin hajjin bara amma suka kasa yin aikin saboda wani dalili da su kai rahoto ga hukumar da ainihin abin da aka biya su bayyana sha’awarsu ta shiga aikin hajjin bana ko kuma a mayar musu da kudi.

Ya bayyana cewa adadin maniyyata mahajjata dari da tamanin da biyar da suka yi cikakken biya a bara ba su yi aikin hajjin ba, sakamakon karancin kujerun aikin Hajji, sakamakon karancin kason aikin Hajji da kasar Saudiyya ta yi.

Daraktan ya bayyana cewa hukumar ta riga ta yi rijistar maniyyata sama da dubu daya don gudanar da aikin Hajjin bana, kuma tun daga nan ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin.