Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Legas za ta fara sayar da fom din aikin Hajjin 2023 a hukumance daga ranar Litinin, 6 ga Fabrairu, 2023.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Prince Anofiu Olanrewaju Elegushi ne ya bayyana haka, a wata sanarwa daga Taofeek Lawal, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a.
Ya kuma yi kira ga maniyyata, musamman wadanda ba su kammala biyan Naira miliyan 2,640,000.00 da aka biya a 2022 ba da su je su cika ta hanyar zuba N1,340,000.00 ta daftarin banki.
Ya ƙara da bayani cewa za a ajiye kuɗin ne ta banki da sunan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Legas, inda ya jaddada cewa hukumar za ta sanar da su idan za a sami wani kari ko raguwar kuɗin idan lokacin ya yi.
Ya kara da cewa jihar ba za ta yi watsi da alkawarin da ta yi a baya ba na kula da su da matukar muhimmanci kafin sayar da fom ga sabbin masu neman zuwa Hajjin bana.
Don haka, ya bukace su da su gaggauta samun sabon fom (kyauta) ta hannun ko’odinetocin kananan hukumominsu domin samun cikakkun bayanai tare da sabunta bayanansu na yanzu.
A cewar sa, bayanan sun haɗa da shekaru da adireshinsu da yanayin lafiyarsu saboda karancin lokacin da Saudiyya ta ba su.