Hajjin bana: NAHCON ta baiwa jihar Kano gurabin alhazai 5902.

0
270

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa Jihar Kano gurbin alhazai dubu 5902 domin zuwa aikin Hajjin bana, 2023.

Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana hakan a yau Asabar yayin ƙaddamar da shirin bita na wannan shekara a Kano.

Alhaji Danbatta ya ce tuni kimanin maniyyata dubu 4 ne suka biya kudin ajiya.

Danbatta, ya ce gwamnatin jihar ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da ayyukan Hajjin da ke tafe ba tare da tangarda ba.

Ya ce hatta aikin Hajjin bara da aka samu matsaloli, jihar Kano ta taka rawar gani inda wanda ya kai ga samun lambobin yabo da dama musamman daga ƙungiya Hajj Reporters.