Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta baiwa Jihar Kogi gurbin alhazai 729 domin gudanar da aikin Hajjin bana.
A sanarwar da Mousa Ubandawaki, Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na NAHCON ya fitar, an yanke baiwa jihar gurbin alhazai 729 ne bayan taron da shugabannin hukumar su ka yi a ranar 3 ga watan Febrairu.