A wani gargaɗi mai ƙarfi, a ranar Lahadin da ta gabata, Kwamitin Hajji na Indiya (HCoI) ya kira wasu bayanai da su ka shafi aikin Hajji na 2023 da ake yadawa a WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta a matsayin na ƙarya da ɓatanci.
Kwamitin Hajji na Indiya shi ne kololuwa mai kula da tafiye-tafiye Hajji, kashe kudi, masauki da sauran shirye-shiryen da suka shafi aikin Hajji na alhazan Indiya.
Kowace shekara ta na gayyatar maniyyata da su cike bayanan su na tafiya aikin Hajji ta yanar gizo.
Sai dai kuma s bana an samu tsaiko ba a fara kiran maniyyatan ba kawo yanzu.
Duk da cewa kwamitin alhazan bai bayyana dalilan da su ka janyo tsaikon ba, amma hakan ya haifar da cece-kuce da bayanan ƙarya a shafukan sada zumunta na wasu mutane.
“An lura cewa bayanai marasa tushe da yaudara da suka shafi sanarwar aikace-aikacen Hajji, kashe kudi, farashi da kuma shirye-shiryen Hajjin 1444 AH – 2023 CE suna yaduwa a WhatsApp da sauran dandamali na kafofin watsa labarun”, in ji shugaban kwamitin Hajj na Indiya, Mohd Yakoob Shekha.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu.
“Wannan bayanin yana haifar da fargaba da rudani a cikin jama’a”, in ji shi.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewa idan lokaci ya yi za a sanar da Maniyyata da su ke su cike bayanai ta yanar gizo.