A yau Talata ne Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta ƙaddamar da cibiyar Horon Aikin Hajji ta Ƙasa, da nufin horar da ma’aikata da ke ɓangaren aikin Hajji da Umrah.
Shugaban NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a wajen bude cibiyar a Abuja.
Hassan ya bayyana cewa, kafa cibiyar zai inganta aikin hajji da umrah da kuma baiwa kasar damar kai wa matsayin ƙasashen duniya a fannin.
Shugaban ya kuma ce cibiyar za ta samar da hanyar koyon sana’o’i da bunkasa kasuwanci ga matasa da kuma zama abar kwatance a duk duniya wajen koyar da aikin hajji da umrah.
Ya kuma ce cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen binciko hanyoyin tattalin arziki da ya yawaita a wannan fanni wanda ’yan kasuwa da matasa masu tasowa za su iya amfana.
“Ina da yakinin cewa cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin Najeriya ta kai ga kuma ci gaba da kasancewa a sahun gaba a harkar Hajji da Umrah ta duniya.
“Za ku yarda da ni cewa duniya na ci gaba cikin sauri a fannin fasaha kuma ya zama wajibi NAHCON ta ci gaba da tafiya tare da wadannan abubuwan da ke faruwa a duniya.
“Saboda haka, ya zama dole mu sake mayar da hankali kan dabarunmu, mu rungumi sabbin ci gaban da aka samu a ICT.