Hajjin 2023: Hukumar alhazai ta Borno ta buƙaci jami’anta da su kaiwa NAHCON kuɗin aikin Hajji kan lokaci

0
636

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Borno, Alhaji Ali M. Bukar ya gana da mahukuntan hukumar, shugabannin sassa, da masu karbar kudaden aikin Hajji na kananan hukumomi a dakin taro na hukumar da ke Maiduguri.

Sakatare, bayan sanar da raba kujerun aikin Hajjin bana ga bangarori daban-daban, ya sanar da taron cewa su tabbatar da sun biya kashi 50% na kudin ajiya da za a baiwa NAHCON a ranar 10 ga Fabrairu 2023 ko kafin ranar.

Don haka ya bukaci wadanda abin ya shafa da su yi iya kokarinsu don ganin sun cika wa’adin da NAHCON ta gindaya.

Ya kuma jaddada cewa za a iya kara wa jihar guraben alhazai amma sai an ga irin ƙwazon hukumar.