Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe, ta gargadi maniyyatan da ke da niyyar biyan kudin Hajjin 2023 ga jami’an da ba amintattu ba don gudun kada a cuce su.
Sakataren zartaswa na hukumar, Alhaji Sa’adu Hassan ne ya bayyana haka a wani taro da jami’an alhazai na kananan hukumomin jihar 11 na jihar Gombe.
Ya kuma shawarci maniyyatan da ke da niyyar zuwa aikin Hajjin da su je kai tsaye wurin hukumar domin biyan kuɗin Hajji da kuma neman bayani.
Hassan ya kuma yi kira ga maniyyatan da ke da niyyar kammala biyan kudaden ajiyarsu domin bin ka’idar da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanya.