YANZU-YANZU: Sheikh Saud Shuraim ya yi murabus a matsayin limamin Masallacin Harami

0
447

Sheikh Saud bin Ibrahim Shuraim ya yi murabus daga matsayin limami na Masallacin Haramin Makkah.

Imam ya ƙi sake sabunta kwantiraginsa da Babban Ofishin kula Da Masallatan Harami biyu tun a karshen 2022, bisa dalilai na kashin kansa.

Amma duk da haka limamin zai iya dawowa limancin wucin-gadi don jagorantar Sallar Tarawihi, wanda za a tabbatar da hakan gabanin watan ramadana.

Kafar labarai ta Inside Haramain a baya ta ruwaito cewa wani fitaccen Imami ya yi murabus.

Majiya mai tushe ta sanar da Inside Haramain cewa Limamin na iya sabunta kwangilar shi kuma ya dawo bisa ga radin kansa.