Hajjin 2023: An umarci maniyyata a Oyo da su fara ajiye miliyan 2.6 kuɗin Hajji

0
332

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Oyo ta kayyade Naira miliyan 2.6 a matsayin kudin ajiya na farko na aikin Hajjin bana na 2023 zuwa kasar Saudiyya.

Shugaban hukumar, Sayed Malik ne ya bayyana haka a sansanin alhazai da ke Olodo a Ibadan a yau Asabar.

Malam Malik musamman ya ce an kayyade adadin kudin ne har zuwa lokacin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana ainihin kudin da za a biya.

Ya ce za a baiwa alhazai 150 da ba su samu gudanar da aikin hajjin 2022 ba, sabo da karancin kujerun da aka ware wa jihar.

Malik ya umarci dukkanin maniyyatan da sau fara biyan kuɗin ta hukumar jin dadin Alhazai ta jihar ta asusun bankin da hukumar ta kebe.

Yayin da ya ke sanar da ‘yan kwamitin kan muhimman batutuwan da suka shafi aikin Hajji na 2023 da aka tattauna a ziyarar farko kafin aikin Hajji a kasar Saudiyya, Malik ya ce NAHCON ta ware kujeru 1441 ga jihar don aikin Hajjin 2023.