Sanwo-Olu ya naɗa sabon shugaban hukumar alhazai ta Legas

0
334

Gwamnan jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo- Olu ya nada Mista Onipede Olayiwola Saheed a matsayin Shugaban hukumar jin dadin alhazai musulmi ta Jihar Legas, bayan tura tsohon shugaban zuwa wata hukuma.

Wasikar nadin, wacce shugaban ma’aikata, Mista Hakeem Muri-Okunola ya sanya wa hannu a ranar Laraba 8 ga Fabrairu, 2023, ta bayyana cewa an yi amfani da kwarewa sansanin malamar aiki wajen amincewa da nadin Onipede.

Shugaban ma’aikatan ya kara jaddada cewa ba shi da tantama cewa sabon shugaban hukumar zai kawo kwarewarsa wajen gudanar da ayyukan hukumar da kuma cewa zai tabbatar da amincewar da Gwamna ya yi masa.

Wasikar ta ce naɗin ya fara aiki nan take.

Onipede, wanda ya fito daga ɓangaren Badagry na jihar Legas mataimakin darakta ne (Admin & HR) a ma’aikatar gwamnati.