Hajjin bana: Jihar Kaduna ta buƙaci maniyyata su fara biyan miliyan 2.5 kuɗin aikin Hajji

0
205

Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya yi kira ga maniyyata aikin hajjin bana a jihar da su ƙara yawan kuɗin ajiyarsu.

Domin ya kai naira miliyan 2.5 mafi ƙarancin kuɗin kujera, kafin ranar 20 ga watan Fabrairun da muke ciki

Dakta Yusuf, ya faɗi hakan ne a lokacin ganawa da manyan jami’an hukumar na ƙananan hukumomin jihar 23.

Babban sakataren ya ce hakan zai taimaka wajen samun damar tura kuɗin zuwa Hukumar Alhazai ta ƙasar da wuri domin tabbatar da yawan kujerun da hukumar Alhazan ta ware wa jihar

Ya ƙara da cewa a yanzu hukumar alhazan ƙasar ta ware wa jihar Kaduna yawan kujeru 5,982 a aikin hajjin bana, yana mai cewa jihar na buƙatar ƙarin kujeru.