Hajjin 2023: Hukumar alhazai ta Jigawa ta ajiye Naira biliyan 1.86 a asusun NAHCON

0
185

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta saka naira miliyan 1,867,362,500 ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON a matsayin biyan kashi 50 cikin 100 na adadin kujerun aikin Hajji da aka ware wa jihar.

Daraktan ayyuka na Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kan shirye-shiryensu na gudanar da aikin Hajjin 2023.

Ya ce hukumar ta kuma karbi kujerun aikin Hajji 1525 da ga NAHCON domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Alhaji Umar Labbo ya bayyana cewa “Hukumar aikin Hajji ta kasa ta kara yawan kujeru da sama da kashi 70 bisa dari idan aka kwatanta da bara, inda jihar ta samu kujeru 630 kacal”.

Ya bayyana cewa tuni hukumar ta raba kujerun ga kananan hukumomi 27 na jihar, inda ya kara da cewa “bayan tsari mai kyau da gaggawa da kuma shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana, hukumar ta cinye kujeru 556.

“An riga an sayar da adadi mai yawa na wannan kujera. Wannan ya hada da 441 da aka biya ta hanyar Adashin Gata na Aikin Hajji a bankin Jaiz.

“Amma an biya 116 a bankin GT. Yayin da ake ci gaba da siyar da kayayyaki, ina da kwarin gwiwar cewa kafin karshen wannan watan, hukumar za ta fitar da dukkan kason da aka ware.”