Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCOH, ta ce a makon farko na watan Maris za ta fara tantance kamfanonin sufurin jiragen sama da za su yi jigilar alhazai a aikin Hajjin 2023.
Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da manema labarai a yau Talata a Abuja.
Hassan ya ce makasudin zaman tattaunawa da manema labarai ɗin shi ne a kara samun fahimtar juna da kwararrun kafafen yada labarai.
Ya ce hukumar na aiki tukuru domin ganin an gudanar da aikin Hajji na 2023 lami lafiya don baiwa alhazan Najeriya damar gudanar da aikin hajjin karbabbe.
“Muna kan aiwatar da wasu abubuwa da yawa bayan haka za mu sami wata hanyar sadarwa mai ma’ana.
” Muna da niyyar fara tantance kamfanonin jiragen sama nan da makon farko na watan Maris. Ina mai tabbatar muku da cewa aikin hajjin bana zai kasance cikin nasara.
“A wannan shekarar za a samu nasara da yardar Allah.”