Saudiyya ta ayyana shekaru 12 a matsayin mafi ƙaranci na yin aikin Hajjin 2023

0
345

Saudiyya ta ce mafi karancin shekarun aikin hajjin bana shi ne shekaru 12 saboda adadin maniyyatan zai koma yadda aka saba kafin lokacin ɓarkewar annobar korona.

Ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta kuma nuna cewa, za a baiwa waɗanda basu taɓa yin aikin Hajji ba fifiko wajen yin rajistar hajjin bans.

Ana iya ba da izinin aikin Hajji ta hanyar kafar sadarwa tta “Absher” daga 15 ga watan Shawwal, 1444AH, wato kasa da watanni biyu kafin lokacin aikin Hajji da zai zo karshen watan Yuni na wannan shekara.

Ma’aikatar ta kara da cewa musulmi masu rike da takardar izinin Hajji ko kuma wadanda ke da izinin zama a kasar Saudiyya ne kadai za a ba su damar gudanar da aikin hajjin na bana.

Tun da fari, ma’aikatar ta gabatar da bukatu hudu na maniyyatan gida da ke son halartar aikin Hajjin shekarar 2023 da kudin da ya kama daga SR,3984 zuwa SR11,841.