Hajjin bana: Shugaban Hukumar Alhazan Kaduna ya fara shirye-shirye da kai ziyarar aiki

0
215

A yunkurin shi na fara shirin aikin Hajjin 2023 da Ummara, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya fara kai ziyarar aiki ga masu ruwa da tsaki, inda ya ziyarci MD na Hukumar Filayen Jirgin Sama, da na Hukumar Shige-da-fice ta ƙasa, wato Immigration na Kaduna.

A tuna cewa jihar Kaduna na da maniyyata kusan dubu 6 da za su je aikin Hajjin bana, wanda adadi ne da ya fi kowanne jiha a Kasar.

Hakan na bukatar shiri akan kari, yayin da aka tattauna muhimman tsare tsare-tsare da kuma shirin da za a tunkara gaba, kamar yadda Mataimaki na Musamman na Shugaban hukumar, Ibrahim Shehu Giwa ya faɗa a wata taiaktacciyar sanarwa da ya fitar.