Hajjin bana: NAHCON ta yaba da shirye-shiryen hukumar alhazai ta jihar Neja

0
349

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta yaba da yadda Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Neja ta shirya tsaf domin gudanar da aikin hajjin 2023.

Shugaban tawagar NAHCON da ta ziyarci jihar, Alhaji Ali Mohammed Ali ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar a Minn, babban birnin jihar,

“Muna nan Jihar Neja ne domin mu gane wa idanun mu tun daga matakin biyan kuɗin aikin Hajji, da hada bayanan maniyyata har zuwa matakin jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki,” a cewar wata sanarwa da Hassan D Idris, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya fitar, wacce ta ruwaito Ali ya na cewa.

Ya ce hukumar ta NAHCON ta kuma tura jami’anta zuwa sassan kasar nan a wani bangare na alkawurran da ta dauka na ganin ba a samu cikas a ayyukan Hajji na 2023 ba.

Alhaji Ali ya kuma yaba wa filin jirgin sama na Minna bisa inganta ayyukansa domin daukar nauyin ayyukan Hajji a jihar.

A nasa ɓangaren, Babban Sakataren Hukumar SPWB na Neja, Alhaji Umar Makun Lapai, wanda ya yaba da ziyarar da jami’an NAHCON suka kai masa, ya bayyana cewa Jihar Neja ta kusan kammala dukkan shirye-shiryenta na ganin an samu gudanar hada-hadar Hajjin bana na 2023 cikin nasara.