Mai kula da sansanin alhazai na Kaduna ya rasu

0
134

Yusuf Hassan Liman, tsohon jami’in rijistar A’alhazai na karamar hukumar Kaduna ta Kudu a Kaduna, kuma mai kula da sansanin alhazan Kaduna a halin yanzu ya rasu.

Wata ‘yar gajeriyar sanarwa da Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ta fitar ta ce Yusuf Hassan Liman ya rasu ne a jiya Alhamis bayan gajeruwar jinya.

Tuni a ka yi ana’izar sa da misalin karfe 4:00 na yamma, a Titin JaAbdulkadir, Unguwar Rimi Kaduna.

Allah Ta’ala Ya gafarta masa, Ya bashi Aljannar Firdausi, ameen.