Kwanan nan ne wasu daliban Jami’ar Harvard su ka gudanar da aikin Ummara a Makka da Madina.
A cewar Malaman Kungiyar Musulmai ta Jami’ar, Khalil Abdur-Rashid da Samia Omar, wadanda su ka shirya tare da jagorantar tafiya Ummarar karo na biyu jami’ar, sun bayyana cewa an samu gagarumar nasara.
Abdur-Rashid da Omar sun jagoranci mahalarta 31 a karon farko na Ummarar a Harvard a 2019.
An ɗauki watanni a na tsara yadda shirin, wanda wani bawan Allah da ya dauki nauyi, ya yi alkawarin tallafa wa dalibai 30 a shekara-shekara don yin wannan tafiya zai kasance.
Shirye-shiryen tafiyar sun haɗa da ƙulla yarjejeniya da hukumomin tafiye-tafiye, samar da biza, hukumar Makaranta da ofisoshin Hukumar lafiya, da ma’aikatun Saudiyya.
Sakamakon ziyarar ta kwanaki 10 na gudana lami-lafiya kuma cikin nasara.