Minista ya buƙaci Saudiyya ta ƙara ma’aikatan aikin Hajji mata

0
354

Ministan harkokin addini, Yaqut Cholil Qoumas ya yi kira ga hukumar kula da ayyukan hajji da umrah da ta kara yawan adadin jami’an hidimomin aikin Hajji mata a ƙasar.

“Musamman ga jagororin ibada. Ga jagororin ibada, ya kamata a samu jagorori mata fiye da yadda maza ke jagoranta,” in ji Ministan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

A cewar Quumas, adadin mata mahajjata ya zarce na maza, don haka a kwai buƙatar a daidaita kason ma’aikatan aikin Hajji na mata daidai da bukatu.

Hakazalika ma’aikatar kula da harkokin addini za ta kuma shirya jami’ai na musamman da za su yi hidima ga alhazai tsofaffi.