Hukumar Alhazai ta Kano ta buƙaci maniyyata su ƙara kashin farko na kuɗin Hajji zuwa N2.5m

0
457

Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano na sanar da maniyyata aikin Hajjin 2023 da su yi kokarin kara kudadensu na kashin farko ya kai Naira Miliyan 2.5

Wannan na kunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da Hadiza Abbas Sanusi, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar ta fitar.

Sanarwar ta ce hukumar ma kira ga maniyyatan ne da su cikasa kuɗin ya kai miliyan 2.5 kafin Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta kayyade kudin aikin Hajji na bana.