Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) za ta fara aikin tantance kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki a cikin watan Mayu.
Shugaban NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan ne ya kaddamar d akwamitin, mai mambobi 36, wanda ke karkashin jagorancin Alh. Abdullahi Magaji Hardawa, kwamishinan aiyuka, ya kaddamar , a ranar Laraba a dakin taro na gidan Hajji, Abuja.
Ya kuma gargade su da su kasance masu himma, adalci da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu, domin alhazai su samu nasarar aikin Hajjin bana
Kamfanonin Jiragen Sama Goma da na masu jigilar kaya uku ne suka nemi jigilar Alhazai da ta Hajjin 2023.
Kamfanonin da su ka nema sun hada da: Aero Contractors, Air peace, Arik Air L.t.d, Azman Air Services, Flynas (wani jirgin da Saudiyya ta kebe), K-impex Airline L.t.d, Max Air L.t.d, Skypower Express Airways, Value Jet, United Nigeria Airline Company Limited.