Hadimin Masallatan Harami guda biyu, Sarki Salman na Saudiyya ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa.
A jawabin sa, Sarkin ya bayyana farin cikinsa ga zababben shugaban kasar bisa dukkan nasarorin da aka samu, inda ya yi fatan Allah ya kara wa gwamnati da al’ummar ƙasar albarka.
Shima a nasa jawabin, Yarima mai jiran gado kuma Firayim Minista Mohammed Bin Salman shi ma ya aike da sakon taya murna ga Tinubu kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Tarayyar Najeriya.
Yarima mai jiran gado, ya bayyana farin cikinsa ga zababben shugaban kasar bisa dukkan nasarorin da aka samu, inda ya yi fatan Allah albarka da ƙasar.