A jiya Litinin ne gwamnatin Pakistan ta amince da kara kudaden aikin Hajji zuwa Rs1.175 ga kowanne mahajjaci – wanda ya karu da kashi 68 cikin dari a kan na shekarar da ta gabata – sannan ta ba da damar fitar da kudaden rabin kason don samun rarar dala miliyan 444 a cikin yayin da ake fuskantar mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki.
Kwamitin daidaita tattalin arziki (EEC) na majalisar ministocin ne ya yanke hukuncin, wanda kuma ya sanya hannu kan kasafin kudin Rufi biliyan 12 don gudanar da kidayar jama’a karo na 7 a daidai lokacin da jam’iyyar Pakistan Peoples Party (PPP) ta nuna adawa da kidaya ta na’ura mai ƙwaƙwalwa.
Bayan gargadin da shugaban jam’iyyar, Bilal Bhutto Zardari ya yi game da barin gwamnati, ministan kasuwanci Syed Naveed Qamar shi ma ya nuna rashin amincewarsa a yayin taron ECC ɗin.
Sai dai shugaban hukumar ta ECV, Ishaq Dar, ya shawarci ministan da ya tattauna da firaminista Shehbaz Sharif.
Sanarwar da ma’aikatar kudi ta fitar ta bayyana cewa ma’aikatar harkokin addini ta gabatar da takaitaccen bayani kan manufofin Hajji na shekarar 2023.
Jimillar kudaden kasashen waje na aikin Hajjin shekarar 2023 sun kai dala miliyan 534 – adadin da ya yi daidai da kashi 14% na asusun ajiyar kudaden kasashen waje na kasar a makon da ya gabata.