Bayan ɗage zaɓe, Hukumar Alhazai ta Kano ta sanar da ci gaba da bitar mako-mako

0
268

Sakamakon dage zabe da hukumar zabe ta kasa ta yi, hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano na sanar da Malaman Bita da Kuma Maniyyatan Jihar Kano cewa za’a ci gaba da yin bitar mako-mako.

Wannan na kunshe ne a sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Hadiza Abbas Sanusi ta fitar a yau Alhamis.

Ta ce za a ci gaba da bitar ne a ranakun Asabar da Lahadi 11 da 12 ga watan Maris kamar yadda a ka saba a cibiyoyin bita 16 da ke fadin jihar.