Hukumar alhazai ta jihar Bauchi ta sanar da masu niyyar zuwa Ummara cewa za su biya Naira miliyan 1,700,000 a matsayin kudin aikin Ummarar Ramadan na bana.
Harilayau, hukumar ta sanya r25 ga watan Maris a matsayin ranar da za a rufe karbar kudin na ummara don bada damar kammala dukkan tsare tsaren tafiya.
A wata sanarwa da Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, Babban Sakataren hukumar ya fitar, hukumar ta yi kira a maniyyatan da waɗanda su ka kashi farko na kuɗin , Naira miliyan 1 da su je shelkwatar don karbar shaidar biyan kuɗin.
“Don haka hukumar ke kira da babban murya ga sabbin Maniyyata da wadanda suka bada kudin ajiyar su N1,000,000 a hukumar, dasu garzayo hedkwatar ta dake kan titin Adamu Jumba daura da kantin Jifatu don karbar shaidar biyan kudin na Banki wato teller na biyan cikakken kudin Umrar su.
“Hukumar ta shirya tsaf don tabbatar da jindadi da walwalar maniyyatar ta na jihar Bauchi tun daga nan gida har zuwa dawowar su.
“Dafatan zaa bada hadin kai,” in ji sanarwar.