Kamfanin sufurin jiragen sama na EgyptAir na kasar Masar, ya sanar da fara jigilar mahajjatan Morocco 3,200 da za su je Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah a shekarar 2023.
Jirgin na farko zai fara jigilar ne ranar Juma’a, a cewar wata sanarwa daga shugaban kamfanin na EgyptAir, Yehia Zakaria, wanda kafar yada labaran Masar ta Alkahira24 ta ruwaito.
Domin aiwatar da shirin, EgyptAir ta kulla yarjejeniya da manyan kamfanonin yawon bude ido a Maroko don tsara jirage 11 tare da Boeing B787-9 Dreamliner mai daukar fasinjoji 309 da Airbus A330-200 mai daukar fasinjoji 268, in ji rahoton.
An shirya tashin jiragen daga filayen tashi da saukar jiragen sama na Casablanca, Tangier, da Fez, tare da filin tashi da saukar jiragen sama na Alkahira kafin isa Jeddah da Madina a kasar Saudiyya.