Saudiyya ta samar da sabon kamfanin sufurin jirgin sama, Riyadh Air

0
243

Yarima mai jiran gado kuma Fira-Minista Mohammed bin Salman, a jiya Lahadi ya sanar a ranar da cewa za a buɗe sabon kafamfanin sufurin jirgin sama “Riyad Air”, wand Asusun Zuba Jarin Al’umma, PIF, ne ya kafa shi.

Sabon jirgin na kasa zai yi amfani da dabarun sanin hanyoyi don yin jigila tsakanin Saudi Arabiya da nahiyoyi uku na Asiya, Afirka da Turai.

Hakan zai ba Riyadh damar zama wata cibiya ga duniya da kuma makoma don sufuri, kasuwanci, da yawon shakatawa.

Yasir Al-Rumayyan, gwamnan PIF ne zai jagoranci Riyadh Air, yayin da Tony Douglas, wanda ya ke da gogewa ta fiye da shekaru 40 a fannin sufurin jiragen sama, da kayayyaki, inda aka nada shi babban jami’in gudanarwa.

Manyan jami’an kamfanin za su hada da ƙwararru a Saudiyya da na ƙasashen duniya.

Kamfanin zai rika aiki daga Riyadh a matsayin cibiyarsa, inda zai kawo sabbin dabarun zamani na tafiye-tafiye da masana’antar sufurin jiragen sama a duniya.

Riyadh Air zai kasance jirgin sama mai daraja a duniya kuma za a gudanar da shi da sabbin fasahohin zamani.

Ana sa ran kamfanin zai kara dalar Amurka biliyan 20 wajen bunkasar tattalin arzikin ƙasarda ba na ɓangaren mai ba, da kuma samar da ayyukan yi sama da dubu 200,000 kai tsaye da kuma wanda ba kai tsaye ba.