Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja za ta fara gudanar da shirin farko na bita na bana a ranakun Asabar 18 da Lahadi 19 ga Maris 2023.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Muhammad Lawal Aliyu ya fitar, hukumar ta bayyana cewa tuni aka hada malaman addinin musulunci domin gudanar da bitar da aka shirya gudanarwa a sansanin alhazai na dindindin da ke Basan Jiwa kusa da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe a Abuja.
Muhammad Lawal ya bayyana cewa, za a gudanar da atisayen ne a matakai domin baiwa maniyyata damar samun fadakarwa kan aikin hajji da kuma sabbin tsare-tsare da mahukuntan Saudiyya da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka bullo da su na aikin hajjin bana.
Jami’in Hulda da Jama’a ya shawarci Alhazan yankin da su ke shirin zuwa aikin hajjin bana da su shiga duk shirye-shiryen da hukumar ta shirya da nufin taimaka musu wajen samun aikin hajji mai karbuwa.
Ya shawarci mahajjata, musamman wadanda suka fara aikin Hajji, da su yi amfani da wannan atisayen da kuma inganta iliminsu na Musulunci kan ayyukan Hajji da shiryarwa mai kyau don samun darajar kudinsu.