Ma’aikaciyar hukumar alhazai ta Kano ta rasu

0
235

Hajiya Fatima Muhammad Kawu, ma’aikaciya a sashen harkokin kuɗi na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rasu.

A wata gajeriyar sanarwa daga ofishin yaɗa labarai na hukumar, marigayiyar ta rasu a jiya Litinin da daddare.

Tuni a ka yi jana’izar ta a yau Talata a Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa Babban Sakataren hukumar, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya nuna alhinin rashin marigayiyar.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da ƴan uwan ta, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata Ya kuma baiwa iyalin ta juriyar rashin ta.