Hajjin 2023: NAHCON ta kafa kwamitin kula da lafiyar alhazai

0
261

A ci gaba da shirye-shiryen Hajjin 2023, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta kafa kwamitin kula da lafiyar alhazai yayin Hajjin na bana.

Kwamitin mai mambobi 17, shi ke da alhakin tantance wa da kuma zaɓo likitocin da za su shiga tawogar jami’an lafiya a matakin ƙasa yayin Hajjin bana.

Bikin ƙaddamar da kwamitin ya gudana ne a hedikatwar NAHCON da ke Abuja.

Da ya ke jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Shugaban NAHCON na ƙasa, Alhaji Zikirullahi Hassan, wanda ya samu wakilcin Kwamishina a hukumar, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa, ya bayyana gamsuwarsa game da mambobin da kwamitin ya ƙunsa, tare da jaddada muhimmiyar rawar da kwamitin zai taka game da aikin Hajji.

Ayyukan da suka rataya a kan kwamitin sun haɗa da:

1. Samar da matakan da za a yi amfani da su wajen aikin kula da lafiya don bunƙasa sha’anin aiki tare a tsakani.

ii. Tantance asibitocin da za a yi amfani da su a Makkah yayin ayyukan Hajji.

iii. Gwajin EMR tare da tabbatar da tsarin ya daidaita da tsare-tsaren ayyukan NAHCON.

iv. Tantancewa da kuma zaɓo waɗanda za su yi aikin kula da lafiya yayin Hajjin bana.

v. Ɗauka da kuma wayar da kan mambobin Tawagar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa (NMT).

vii. Ɗaukar bayanai da shirya bizar ma’aikatan lafiya.

viii. Tabbatar da rijistar kayayyakin kula da lafiya a tsarin bin diddigi na ‘E-track system’.