Sarkin Zazzau ya ƙaddamar da bitar Hajji bana a Kaduna

0
447

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya ƙaddamar da shirin bitar Hajjin 2023 ga maniyyatan jihar Kaduna.

Sarki Bamalli ya ƙaddamar da shirin ne a ranar Alhamis a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, a babban zauren taron Sakatariyar Gambo Sawaba da ke Dogarawa.

Bamalli ya ce shirin na da muhimmanci saboda zai taimaka wajen ɗora maniyyatan jihar a kan turbar da ta dace game da aikin Hajji.

Don haka, a cewar sa, ya zama wajibi waɗanda aka shirya shirin domin su da su maida hankali wajen riƙe abubuwan da za a koyar da su.

Daga nan ya yi kira a gare su da su guji duk wani abu da ka iya taɓa mutuncinsu da ma mutuncin ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, Basaraken ya shawarci maniyyatan da su tabbatar da bayanan da ke kan ‘passport’ ɗinsu sun daidaita da na sauran takardunsu don kauce wa fuskantar akasi.

Tun da fari da yake jawabi, Sakataren hukumar, Dr Yusuf Arrigasiyyu, ya ce an ƙaddamar da shirin ne da zimmar koya wa maniyyata yadda ake aiwatar da aikin Hajji a sauƙaƙe.

Ya ce tun a watan Fabrairu suka binciko malaman da za su ilimantar da maniyyatan daidai da karantarwar Annabi Muhammad (SAW).

Ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Honarabul Ibrahim Usman, bisa ƙoƙarin da ya yi wajen gina sabon zauren taron maniyyata.

Ya ƙara da cewa, kujerun Hajji 5,982 jihar Kaduna ta samu daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) don Hajjin bana.

Mahalarta taron sun haɗa jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi da hukumar NAFDAC da sauransu.