Duk kujerun aikin Hajji 436 na Ondo sun ƙare

0
189

Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta ware wa jihar Ondo kujerun aikin Hajjin bana guda 436.

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Alhaji Zikrullah-Chandy Adam ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a Akure.

Adam, wanda ya bayyana aikin Hajjin 2022 a matsayin wanda aka yi shi na farko bayan annobar COVID-19, ya ba da tabbacin samun ci gaba don tabbatar da ayyukan Hajji na 2023 ba tare da matsala ba.

Maniyyatan jihar sun riga sun cike dukkan kujeru 436 da aka baiwa jihar daga cikin kujeru 96,000 da gwamnatin Saudiyya ta ware wa Najeriya.

Shugaban hukumar ya ce hukumar ta dauki matakin da ya dace domin ganin an gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.

“Hukumar ta shirya kai ziyara ta biyu zuwa Saudiyya mako mai zuwa, gabanin gudanar da aikin Hajji,” inji shi.

Ya ce kowane mahajjaci ya ajiye kudi na farko na Naira miliyan 3 domin gudanar da aikin ya kara da cewa, za a iya biyan kudaden da ake biya a tsakanin N2.8million zuwa N3.2million.