Hajjin bana: Za mu tabbatar maniyyatan Neja sun tashi daga Mina zuwa Saudiya – Hukumar alhazai

0
194

Gwamnatin jihar Neja ta yi alkawarin yin duk mai yiwuwa na wajen ganin cewa maniyyatan jihar sun tashi daga filin jirgin sama na Nuna, babban birnin jihar a aikin Hajjin bana.

Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Neja, Alhaji Umar Makun Lapai ne ya bayyana haka a lokacin da wasu jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NACA, ta kasa daga Abuja suka ziyarci filin jirgin sama na Minna.

Manufar ziyarar duba kayayyakin da jami’an hukumar ta NCAA suka kai a filin jirgin ita ce domin sanin yanayin wasu cibiyoyi a filin jirgin da kuma gano wuraren da ke bukatar kulawar gaggawa daga gwamnatin tarayya ko ta jiha kafin a fara aikin Hajjin 2023.

Wuraren da jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasa su ka duba a filin tashi da saukar jiragen sama na Minna, sun hada da; Tsaro, titin jirgin sama, injunan tantance matafiya, zauren tashi da duk kewayen filin jirgin sama.

A bara dai ba a amince tashin alhazai sfilin jirgin sama na Minna zuwa aikin Hajji a Saudiya ba.