Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Edo, Sheikh Ibrahim Oyarekhua, ya bayyana cewa maniyyata 335 ne suka biya kudin aikin hajjin bana zuwa Makkah da ke kasar Saudiyya don aikin hajji.
Sheikh Ibrahim ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar City & Crime akan shirye shiryen hukumar na aikin Hajjin 2023.
“Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta baiwa jihar Edo kujeru 274 amma a halin yanzu 335 sun biya kudin aikin hajjin bana,” inji shi.
Ya ce adadin maniyyatan da suka biya ya zarce adadin kujeraru da aka ba jihar da 61.