Shugaban Hajj Reporters ya isa Saudiyya don ganin yadda Nijeriya ke shirye-shiryen Hajjin 2023

0
136

Shugaban Kungiya Mai Zaman Kanta da ke kawo rahotannin kan Hajji da Ummar, wato Independent Hajj Reporters (IHR), Ibrahim Mohammed, ya isa kasar Saudiyya domin sa ido kan shirye-shiryen da kamfanonin yi wa alhazai hidima da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta dauka, domin samar da ayyuka daban-daban ga alhazan Najeriya a lokacin aikin Hajjin 2023.

A jiya Juma’a ne Alhaji Mohammed ya tashi daga Najeriya a cikin jirgin Ethiopian Airline zuwa Jeddah ta Addis Ababa.

“Mun gudanar da nazari sosai kan ayyukanmu dangane da yadda muke sa ido kan ayyukan masu ruwa da tsaki, inda kuma muka ga cewa da zama a gida Najeriya kaɗai don bayar da rahoto ba zai gamsar ba, don haka akwai bukatar mu yi tattaki mu ganewa idon mu don ganin shirye-shiryen da ake yi na gudanar da ayyuka da hidimomi ga alhazai baƙin Allah daga Nijeriya,” in ji Alhaji Ibrahim bayan ya sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jedda.

Shugaban na IHR ya kuma ce “shugabannin IHR ne su ka ga bukatar in duba masauki, ciyarwa da kuma hidimar zaman Minna da ake yi sannan in kai rahoto ga maniyyatan Najeriya masu niyya kan abin da za su yi tsammani a wannan shekara”.

Ya kara da cewa, ya kamata kungiyoyin farar hula irin su IHR, su rika gudanar da irin wadannan tafiye-tafiye na kashin kansu da kansu ta yadda za a kare yancin alhazai da kuma tabbatar da cewa sun amfani kuɗin da su ka biya.

“Za mu yi nazari sosai kan duk shirye-shiryen da masu ba da hidimomi da hukumomin Saudiyya ke aiwatarwa tare da bayar da rahoto ga jama’ar Najeriya, wannan na yi imanin zai taimaka wa tsarin sosai da inganta ayyukan,” in ji Alhaji Ibrahim.