Ba a yarda a yi ummara sau biyu a cikin watan Ramadan ba — Saudiyya

0
377

Ma’aikatar Hajji da Umra ta jaddada cewa, ba a yarda mutum ya yi ummara sau biyu a cikin watan Ramadan ba, inda ta ce kowa na da damar yin ta sau daya ne kawai.

Wannan yunkuri dai shi ne don bada dama ga dukkan sauran alhazai masu sha’awar yin aikin ummara a cikin wata mai alfarma da za su iya gudanar da ibadar cikin sauki da nishadi.

Ma’aikatar ta jaddada wajabcin ba da izini ta amfani da manhajar Nusuk don gudanar da aikin Umrah, baya ga muhimmancin sadaukar da lokacin da aka kayyade.

Sai dai kuma ma’aikatar ba bada zaɓin canja ranar da maniyyaci zai yi Umrah ba a manhajar, inda ta yi bayanin cewa amma mahajjata za su iya goge ranar da aka sanya musu ta yin ummara a manhajar ta Nusuk, kafin shigar da lokacin izini, sannan a sanya musu wata ranar.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa ana sanya ranar yin ummara ga maniyyaci lokaci zuwa lokaci, inda ta ce idan mahajjata ba su sami ranar da su ke buƙata ba, to za su iya bincika wata ranar da ta yi musu su dauke ta domin gudanar da aikin na ummara.