Duk wanda aka kama ya na bara a Harami zai ɗanɗana kuɗarsa – Saudiyya

0
183
TOPSHOTSMuslim pilgrims perform the final walk (Tawaf al-Wadaa) around the Kaaba at the Grand Mosque in the Saudi holy city of Mecca on November 30, 2009. The annual Muslim hajj pilgrimage to Mecca wound up without the feared mass outbreak of swine flu, Saudi authorities said, reporting a total of five deaths and 73 proven cases. AFP PHOTO/MAHMUD HAMS (Photo credit should read MAHMUD HAMS/AFP/Getty Images)

Daraktan Tsaron Al’umma na Saudiyya, Laftanar Janar Muhammad Al-Bassami ya bayyana cewa, masu aikata munanan aiyuka da su ka haɗa da barace-barace a Masallacin Harami da harabarsa da ke birnin Makkah za su ɗanɗana kuɗarsu.

Al-Bassami ya yi wannan jawabi ne a taron manema labarai da kwamandojin jami’an tsaro na Umrah a cibiyar Unified Operations Centre 911 da ke Makkah a ranar Talata.

Al-Bassami, tare da wasu manyan jami’an tsaro sun yi magana game da tsare-tsare da shirye-shiryen ma’aikatar harkokin cikin gida na kakar Umrah ta bana a watan Ramadan.

Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farar hula, Manjo Janar Hamoud Al-Faraji da Mataimakin Darakta Janar na Fasfo Manjo Janar Saleh Al-Murabba su ma sun halarci taron manema labaran.

Al-Bassami ya ce, shirin tsaron Umrah na shekara ta 1444 ya kunshi muhimman batutuwan tsaro kamar yadda ake gudanar da taron jama’a, da kula da zirga-zirgar ababen hawa, da samar da ayyukan jin kai, baya ga tallafawa da karfafawa bangarorin da ke shiga cikin aiwatar da shirin, da samar da wadanda suka dace da yin aikin.