Jihar Bauchi ta bayyana aniyarta ta samar da mafi kyawun masaukai ga alhazanta, yayin da a ke fama da karancin ingantattun masaukai a garin Makkah.
Babban Sakataren Hukumar Alhazai na jihar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya tabbatar da hakan daga kasar Saudiyya a lokacin da ya jagoranci tawagar da ke duba masaukan alhazai a Makkah da duba kan tsarin abinci ga maniyyatan jihar a matsayin wani sharadi na tattaunawa.
Ya ce ziyarar ta shirye-shiryen aikin Hajji ita ce ta samar da daidaito wajen samun nasarar aikin Hajjin 2023, kamar yadda wata sanarwa da Muhammad Sani Yunusa, Jami’in Yada Labarai na hukumar ya fitar ya bayyana.
Ya yi nuni da cewa, gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ta ba da fifiko ga jin dadin alhazai ta yadda za su samu damar halartar aikin Hajji mai karbuwa da kuma samun darajar kudinsu.
Da ya ke kokawa kan yadda ake ci gaba da rusa gidaje da dama da mahajjatan Najeriya ke amfani da su a baya, kasancewar wani shiri na ci gaban kasar Saudiyya, Imam Abdurrahman ya tabbatar da cewa Bauchi za ta ci gaba da rike matsayinta na samar da mafi kyawun masauki ga maniyyatan.
Don haka ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga maniyyatan da su ka ajiye kaso farko na kudin Hajji da bai kai Naira miliyan 2.5 ba da su cika, yayin da hukumar NAHCON za ta sanar da ƙayyadajjen kudin aikin Hajjin bana.
Ya kuma shawarci wadanda suka yi ajiya har zuwa Naira miliyan 2.5 kuma har yanzu basu samu takardar rijistar ta yanar gizo ba da su garzaya cibiyar da suka biya domin karbar fom din nan take sannan su dawo da shi bayan sun cike.